A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a safiyar yau Litinin, wadda ta yi daidai da ranar haihuwar Imam Ali (AS) da kuma cika shekaru shida da shahadar Janar Qassem Soleimani, ya bayyana cewa Adalci da Takawa na Imam Ali su ne abubuwa biyu da ƙasa tafi buƙata kuma mafi muhimmancin siffofin da ake buƙata wajen jagoranci tare da jaddada buƙatar kasancewa cikin faɗakarwa da ƙarfafa haɗin kan ƙasa domin fuskantar "Yaƙin Ruwan Sanyi" (Soft War) na makiya. Ya bayyana cewa: "Wannan yaƙi da aka gina shi akan 'ha'inci, ƙarya, cin mutunci, da jita-jita', daidai yake da yaƙin da makiya gwamnatin Imam Ali (AS) suka ƙaddamar bayan sun sha kashi a fagen fama, da nufin hana shi cimma manufofinsa na adalci."
Jagora Ayatullah Khamenei ya bayyana ranar haihuwar Shugaban Muminai (Imam Ali) a matsayin wata rana ta musamman a tarihi, duba da inda aka haife shi — wato cikin Dakin Allah (Ka'aba) — da kuma girman wanda aka haifa. Ya ƙara da cewa: "Daga cikin siffofinsa na musamman da ba su da tamka, a yau muna matukar buƙatar siffofi guda biyu, wato 'Adalci da Taƙawa'. Dole ne mu sanya Shugaban Masu Takawa (Imam Ali) a matsayin abin koyi, mu yi tafiya zuwa ga waɗannan kololuwar guda biyu da yake kai. Tabbas, mun samu ci gaba a wannan tafarkin, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba kafin mu kai ga inda ya kamata mu isa."
Jagora ya yi bayani dalla-dalla kan hanyoyi daban-daban da Shugaban Muminai, Ali bin Abi Talib (AS), ya bi wajen tabbatar da adalci, inda ya ƙara da cewa: "Wani lokacin (Imam Ali) yana tabbatar da adalci ne ta hanyar 'tausayi, hidima ga raunana da iyalai marasa gata'; wani lokacin kuma ta hanyar 'Zulfiqar (takobinsa) da tsananin da Allah ya umarta' (ga azzalumai); wani lokacin kuma ta hanyar 'magana mai ratsa zuciya, hikima, da bayani (tabyin)'."
Jagora ya bayyana Shugaban Muminai (Imam Ali) a matsayin tushen "Jihadin Bayani" (Jihadut Tabyin), inda ya ƙara da cewa:
"Umarnin shugabanci da ya aike wa Malik al-Ashtar cike yake da ma'anoni da ka'idojin da suke tabbatar da adalci a aikace."
Jagora Ayatullah Khamenei, yayin da yake bayyana hanyoyin da Imam Ali (AS) ya bi wajen nuna Takawa, ya ƙara da cewa:
"Wani lokacin Shugaban Muminai yana bayyana takawa ne a cikin mihrabin bauta, ta hanyar Sallah da kankan da kai ga Ubangiji, har sai hakan ya sanya mala'ikun Al'arshi mamaki da sha'awa; wani lokacin kuma yana nuna ta ne ta hanyar haƙuri, yin shiru, da barin haƙƙinsa domin kare haɗin kan Musulmi da hana rarraba a tsakaninsu; wani lokacin kuma, ta hanyar sadaukar da kai a cikin matsananciyar yanayi kamar daren Laylat al-Mabit da yaƙe-yaƙen Manzon Allah (SAWA)."
Yayin da yake nuni da mahimmancin bin tafarkin taƙawa na Shugaban Muminai (Imam Ali) ga daukacin mutane, musamman ma shugabanni da jami'an gwamnati, ya kara da cewa:
"Haka nan, 'Adalcin Alawiyye' shi ne mafi girma kuma mafi gaggawar buƙatar ƙasar nan a yau. Sabanin yadda mabiya Shi'a suka kasance a tsawon tarihi (lokacin da ba su da iko), mu a yau ba mu da wani dalili ko hanzari na rashin bin diddigi da tabbatar da adalci; domin kuwa wannan gwamnati tamu ta 'Jamhuriyar Musulunci ce kuma tsarin Alawiyye ne'."
Yayin da yake bayyana abubuwan da ke zama shinge ga tabbatuwar Adalci da Taƙawa, Jagoran ya ce: "Wani lokacin tsoro, wani lokacin shakka, wani lokacin kuma kulla alakar abokantaka (son zuciya ga dangi ko abokai), wani lokacin kuma yin la'akari da abin da makiya za su ce, su ne suke hana aiwatar da aiki yadda ya kamata. Amma dole ne a matsa zuwa ga fadada adalci da taƙawa ba tare da yin wani la'akari na banza da ba shi da amfani ba."
Yayin da yake jan hankalin al'umma da jami'an gwamnati zuwa ga wani muhimmin darasi a rayuwar Shugaban Muminai (Imam Ali), Jagoran ya ce: "Dole ne a kula da cewa, Shugaban Masu Takawa (Imam Ali) ya kasance mai nasara kuma mai cin nasara a dukkan yaƙe-yaƙen soja da aka yi a zamanin Manzon Allah (SAWA) da kuma shekarun mulkinsa; sai dai hanyoyi daban-daban da maƙiya waɗanda suka sha kashi a fagen fama suka bi na yaudara da sanyaya gwiwar mutane, su ne suka hana cimma manufofin Imam Ali (AS) a lokuta da dama."
Jagoran Juyin Juya Hali ya bayyana cewa, yaɗa jita-jita, amfani da ƙarya, yaudara, kutse, da sauran hanyoyi makamantan su waɗanda a yau ake kira "Yaƙin Ruwan sanyi" (Soft War), su ne manufofin da makiya Shugaban Masu Takawa (Imam Ali) suka bi domin cire wa mutane karsashi da kuma dasa shaku a cikin al'ummar wancan lokacin. Ya ce: "Idan mutane suka yi sanyi (suka raunana), cimma manufofi zai gagara; domin a bisa tsarin Allah (Sunnar Allah), nasara tana hannun mutane kuma ta hannunsu ne ake aiwatar da ita."
Jagora Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa burin makiya a cikin "Yaƙin Ruwan sanyi" (Soft War) shi ne cire wa mutane karsashi, sanya su yanke ƙauna (fidda tsammani), da kuma dasa shaku a tsakanin al'umma. Ya ce: "Kamar yadda aka yi a zamanin Shugaban Muminai, inda aka yi amfani da yaɗa jita-jita da ƙarya domin sa mutane su yi zargin shugabancinsa, a yau ma ana sake yin waɗannan dabarun daidai yadda suke. Sai dai al'ummar Iran ta nuna cewa, a kowane fage mai wahala da kuma duk inda ake buƙatar kasancewarsu da taimakonsu, suna tsaye da ƙarfi, kuma hakan yana sa makiya su fidda tsammani."
Jagora ya bayyana cewa karsashi da kwazo mai ƙarfi na al'ummar Iran shi ne babban abin da ke tada wa makiya hankali, inda ya ƙara da cewa: "Ɗaya daga cikin makaman makiya da wasu mutane marasa kishin ƙasa ko kuma gafalallu a fagen 'Yaƙin Ruwan sanyi', shi ne inkarin abubuwan da al'ummar Iran ta mallaka da kuma iyawarta. Domin kuwa gafala daga ƙarfin ƙasa shi ne ke share fagen wulaƙanci da kuma miƙa wuya ga makiya."
Haka kuma, ya bayyana tura tauraron ɗan adam guda uku zuwa sararin samaniya a rana guda, da kuma ci gaba mai ban mamaki a fannoni daban-daban na kimiyyar ƙasar — kamar su hawa-faɗarin (aerospace), fasahar halittu (biotechnology), likitanci, magani, nano-technology, da masana'antun tsaro da makami mai linzami — a matsayin misalan manyan ayyuka na al'umma da matasa masana na Iran. Ya ce: "Makiya, kuma abin takaici har da wasu a cikin gida, suna ɓoye waɗannan manyan nasarori waɗanda aka samu a tsaka da takunkumin tattalin arziki, kuma ba sa barin labarin ya isa kunnen mutane."
Jagora Ayatullah Khamenei ya ƙara da cewa: "Abin da ya sa makiya suka nemi a tsagaita wuta, kuma bayan haka suka aika saƙon cewa ba sa son yaƙi da ku, shi ne ƙarfi da iyawa na al'ummar Iran. Tabbas, mu ba mu da wani amincewa ko yarda da maganar makiya ƙasƙantattu, masu yaudara kuma maƙaryata."
Yayin da yake nuni da cewa matsakaicin shekarun masanan da suka shiga aikin harba taurarin ɗan adam guda uku kwanan nan shekaru 26 ne, ya bayyana hakan a matsayin misali na babban arzikin albarkatun ɗan adam da al'ummar Iran take da shi. Ya ce: "A lokacin da wancan mai maganar banza na Amurka, idan yana magana game da al'ummar Iran, yakan yi wasu munanan kalami, sannan ya biyo baya da yaudara da alkawuran ƙarya. Amma abin farin ciki shi ne, a yau al'ummar Iran — har ma da ma duniya baki ɗaya — sun riga sun san Amurka, kuma asirinsu ya tonu a idon duniya."
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa, gane ainihin dabi'ar makiya wani babban rabo ne (nasara ce), inda ya ƙara da cewa: "A lokacin Yaƙin Kwanaki 12, mutane da kansu sun ga ainihin fuskar Amurka. Hatta waɗanda suke ganin cewa hanyar magance matsalolin ƙasar ita ce tattaunawa da su (Amurka), sun fahimci cewa a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawar, gwamnatin Amurka tana can tana shirya yaƙi."
Jagora ya bayyana cewa kasancewa cikin faɗakarwa ga "Yaƙin Ruwan sanyi" (Soft War) da kuma dabarun makiya na dasa shakku da yaɗa jita-jita wani abu ne da ya zama dole. Ya yi nuni da biliyoyin daloli da makiya ke kashewa domin yaɗa ƙarya a cikin Iran ta hanyar gidajen talabijin da kafofin watsa labarai, inda ya ce: "Manufarsu ita ce raunana ƙasar nan da kuma wargaza haɗin kan ban-mamaki da al'umma suka nuna a lokacin yaƙin kwanaki 12. Saboda haka, mafi muhimmancin abu shi ne lura da gabar makiya, da ƙarfafa haɗin kai da amincewa a tsakaninmu, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana: 'Masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu'."
A wani ɓangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da tarukan da ƴan kasuwa suka yi a makon da ya gabata, inda ya ce:
"Kasuwa da ƴan kasuwa suna cikin ɓangarori mafi aminci ga tsarin mulki da juyin juya halin Musulunci, kuma mun san hakan sosai. Saboda haka, ba za a taɓa barin wasu su yi amfani da sunan kasuwa ko ƴan kasuwa domin fito-na-fito da Jamhuriyar Musulunci ba."
Jagora ya bayyana cewa korafin da yan kasuwa suka yi game da faduwar darajar kudin kasa (Rial), wanda ke janyo rashin tabbas a harkokin kasuwanci, magana ce ta adalci da gaskiya, inda ya kara da cewa: "Dan kasuwa gaskiya yake fada cewa a karkashin wadannan sharudda ba zai iya yin kasuwanci ba; wannan lamari ne da jami'an kasar ma suka yarda da shi, kuma Shugaban Kasa mai girma da sauran manyan jami'ai suna kokarin ganin sun magance wannan matsalar."
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya ci gaba da cewa:
"Tabbas, a cikin wannan matsalar ma akwai hannun makiya; rashin tabbas da tashin farashin kudaden kasashen waje ba kakkautawa — wanda ke sanya yan kasuwa cikin rudani — ba abu ne na haka siddan ba. Saboda haka, dole ne a dauki matakai daban-daban domin dakatar da hakan, kuma jami'ai suna kan kokarin yin hakan a halin yanzu."
Jagora Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa korafin da 'yan kasuwa suka yi kan wannan matsala magana ce ta gaskiya, amma ya ce: "Abin da ba za a amince da shi ba, shi ne wasu mutane da makiya suka tunzura ko kuma hayar su aka yi, su fake a bayan 'yan kasuwa suna rera taken da suka saba wa Musulunci, da adawa da Iran, da kuma adawa da Jamhuriyar Musulunci."
Ya ci gaba da jaddada cewa "korafi ya dace, amma korafi ya bambanta da tada hargitsi", inda ya ce: "Dole ne jami'ai su zauna su tattauna da masu korafi (domin magance matsalarsu), amma yin magana da mai tada hargitsi ba shi da amfani; a maimakon haka, dole ne a tsawatar masa tare da mayar da shi mazauninsa (domin tabbatar da doka da oda)."
Jagoran ya bayyana cewa babban aikin makiya a kowane lokaci shi ne neman dama don cutar da ƙasa. Yayin da yake nuni da cewa jami'an gwamnati suna kan fagen aiki, ya bayyana cewa: "Abin da ya fi muhimmanci shi ne kasancewar daukacin al'umma cikin shiri, da kuma ƙarfafa abubuwa kamar imani, ikhlasi, da aiki na gari; waɗannan su ne abubuwan da suka mayar da (Shaheed) Sulaimani ya zama Sulaimani." Ya ci gaba da cewa babban makamin shi ne rashin nuna halin ko in kula (rashin damuwa) a gaban "Yaƙin Ruwan sanyi" da jita-jitar makiya. Dole ne a tsaya tsayin daka tare da kare mutuncin ƙasa da dukkan ƙarfi a gaban duk wani matsin lamba da makiya suke son ɗora wa jami'ai, gwamnati, da al'umma.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: "Ba za mu taba yin baya-baya ko raunana a gaban makiya ba. Tare da dogaro ga Ubangiji da kuma tabbacin goyon bayan mutane, za mu tilasta wa makiya durƙusawa."
Jagora Ayatullah Khamenei, a wani ɓangare na jawabin nasa, ya yi nuni da daidaituwar ranar zagayowar shahadar babban gwarzo Shaheed Haj Qassem Sulaimani da ranar 13 ga watan Rajab (ranar haihuwar Imam Ali), inda ya ce:
"Siffofi guda uku, wato 'Imani', 'Ikhlasi', da 'Aiki', su ne manyan siffofin wannan shahidi abin ƙauna, wanda ake kallonsa a matsayin cikakken mutum (insan kamil) a zamaninmu."
Jagoran ya bayyana cewa imani mai zurfi ga Ubangiji da taimakonSa, tare da imani kan manufa, su ne siffofin da suka fi fice a tattare da "Janar ɗin Zuciyoyi" (Sardar Dil-ha). Ya ƙara da cewa: "Haj Qassem mutum ne mai cikakken ikhlasi ga Allah; ba ya yin komai don neman suna ko don mutane su yaba masa."
Jagora ya yaba da yadda Shahid Sulaimani yake halartar duk inda ake buƙatarsa. Ya bayyana cewa:
Sabanin wasu mutanen da suke da fahimta da iya magana amma ba su daukar mataki na aiki, Haj Qassem yana sahun gaba a kowane fili.
Ya halarci fafatawa da miyagu a Kerman, ya jagoranci dakarun Kudus, ya kare wurare masu tsarki (Haram), kuma ya murƙushe ƙungiyar ISIS (Da'esh).
Jagoran ya nuna yadda Janar Sulaimani ya yi tasiri na musamman a cikin muhimman al'amuran siyasa na yankin Gabas Ta Tsakiya. Sannan ya jaddada cewa Haj Qassem ya ba da muhimmanci sosai wajen horarwa da rainon jarumai da sojoji da suke ƙarƙashinsa. Wannan ya sa a yau mutane daga wurare masu nisa da ma sauran ƙasashe suke ziyartar kabarinsa cikin girmamawa.
A ƙarshe, Jagoran ya yi ishara ga iyalan shahidan yaƙin kwanaki 12 da suka halarci taron. Ya ce:
"Wannan zama an yi shi ne don karramawa da girmama dukkan shahidan tsaron ƙasa na wannan yaƙi da iyalansu — kama daga manyan hafsoshi masu kishin jihadi, masana kimiyya masu ƙwazo, da sauran dukkan shahidai."
Jagoran ya jaddada cewa sunayen waɗannan shahidai za su dawwama a tarihi, kuma ya zama dole mu yi amfani da albarkar waɗannan sunaye masu daraja.
Your Comment